Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wani Akaninyene Okokon bisa zarginsa da lakadawa ‘yarsa ‘yar shekara 16, Abasiono Akaninyene Sunday duka tsiya inda ya kashe ta har lahira.
Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Olatoye Durosinmi, ya ce jami’an hedikwatar shiyya ta Ikot Ebo sun kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun sahihan bayanai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane Sama Da 200 Sun Rasa Muhallansu Yayin Da Wata Gobara Ta Tashi
Durosinmi ya yi magana ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane 195 da rundunar ta kama bisa laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, sata, kungiyoyin asiri da fasa bututun mai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ikot Akpanabia, Uyo.
“An kama mutane 196 da ake zargi da laifuka daban-daban da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, satar yara, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, lalata bututun mai, kungiyar asiri, da dai sauransu.
“A ranar 11 ga watan Disamba, 2022, bisa dogaro da sahihan bayanai, jami’an hedikwatar ‘yan sanda ta Ikot Ebo sun kama wani Akaninyene Sunday Okokon.
“Ya yi wa diyarsa, Abasiono Akaninyene Sunday mai shekaru 16 duka har ta suma, saboda tayi amfani da layin sa na SIM wajen kiran saurayinta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an garzaya da wanda abin ya shafa zuwa prayer house da ke kauyen Ikot Iya, maimakon a kai ta asibiti.
“Wasu daga cikin wadannan mutanen an gurfanar da su a gaban kotu, ana ci gaba da bincike kan wasu, yayin da wasu kuma an bayar da belin” ‘yan sanda.
“Ya zuwa yanzu, an ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, an kwato bindigogin gida guda 18 da sauran bindigogi, yayin da aka kwato motoci 11 da aka sace a lokuta da wurare daban-daban a jihar.
“A ranar 16 ga watan Disamba, da misalin karfe 2 na rana, a kauyen Inua Eyet Mkpanak a karamar hukumar Ibeno, jami’an hukumar bincike na musamman sun kama wasu ‘yan kungiyar da suka kware wajen lalata bututun man fetur.”
Yayin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai, Akaninyene Sunday Okokon wanda ake zargi da lakada wa diyarsa duka har lahira, ya ce ba zai iya kashe diyar tasa ba da gangan.
Kalamansa na cewa ban hallaka ta ba:
Ya ce ‘yarsa ta rasu ne sakamakon ciwon ciki.
“Na yi wa ‘yata duka amma ba ta mutu ba lokacin da na daina dukanta.
Ya kara da cewa “Bayan na daina dukanta ne mahaifiyarta ta gaya min cewa (‘yata) tana cikin bacin rai.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Sake nada Adeyeye A Matsayin Shugabar Hukumar NAFDAC
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta nadin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin babbar daraktar Hukumar Kula da ingamcin Abinci da Magunguna ta kasa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Juma’ar nan.