Akwai fargaba a tsakanin ‘yan uwa kwamishinan harkokin mata na jihar Kano, Dr Zahrau Muhammad Umar, sakamakon bacewar danta mai shekaru 24, Abdulrahman Abdu Usman.
Jaridar City News ta ruwaito cewa Abdulrahman ya bace kusan kwanaki 15 kuma har yanzu ba a tabbatar da yadda lamarin ya faru ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ya bar gidansu da ke Kano a ranar 17 ga watan Janairu zuwa Katsina inda yake gudanar da aikin yi wa kasa hidima watau (NYSC) kuma tun daga lokacin duk kokarin gano inda yake abun ya citira, saboda ba a iya samunsa ta wayar salula ba.
Hakazalika yan uwansa sun tabbatar da cewa Abdulrahman bai isa jihar Katsina ba.
Amma Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tuni aka sanar da jami’an tsaro a jihar kuma suna aiki ba dare ba rana domin samun nasara, gani inda yake.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishiniyar ta ce sun shafe kwanaki ba suga saurayin ba.
Wata majiya mai tushe da ta yi magana da jaridar City News ta tabbatar da cewa babu wanda ya tuntubi dangin kan yiwuwar sace Matashin domin neman kudin fansa.
Yawan mutanen da aka bayar da rahoton bacewar na karuwa a fadin jihar ta Kano, in ji City News.
A kwanakin baya ne wani tsohon kakakin majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa ya biya Naira Milliyan 40, domin a sako mahaifiyarsa Hajiya Zainab Danja da aka yi garkuwa da ita.