By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama Rochas Okorocha, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
EFCC ta dauke Okorocha daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin ranar Talata.
Da Dumi-dumi: 2023: Dino Melaye Ya Rasa Tikitin Tsayawa Takarar Sanata A Jihar Kogi
Tun da farko dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta mamaye gidan tsohon gwamnan jihar Imo a kokarin da take yi na cafke shi.
An ce an jiyo karar harbe harbe a lokacin da aka kai farmaki gidan Okorocha.
EFCC ta bayyana cewa Okorocha ya tsallake belinsa na mulki da aka ba shi kuma ya ki amsa gayyatar da ta yi masa.
Ana zargin Okorocha da karkatar da kadarorin jama’a na Naira biliyan 2.9 a lokacin da yake gwamnan jihar Imo.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Okorocha a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar 24 ga watan Junairu, 2022.
Comments 1