Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ta fara taronta, kamar yadda jaridar PUNCH ta tabbatar.
An fara taron ne da misalin karfe 12:40 na yammacin ranar Litinin din nan.
Wani mamba a majalisar zartaswar ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu wanda ba a bayyana sunansa ba. Majiyar ta ce “An fara taron ne kawai“.
A baya dai jaridar Dimokuradiyya ta bayar da rahoton yadda ASUU ta kira taron gaggawa na majalisar zartaswarta NEC sakamakon biyan albashi na rabin wata da gwamnati ta biya.
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Zirga-zirgar Jirgin Kasan Kaduna-Abuja
Gwamnatin tarayya a ranar Litinin din nan ta ce aikin jirgin kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna zai dawo cikin wannan wata na Nuwamba.
Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ba da katin shaida na ma’aikatar sa a Abuja.