Wata tankar mai ta fashe a harabar gidan man da ke Umuahia, babban birnin jihar Abia da safiyar Asabar.
Mazauna hanyar Aba da ke babban birnin jihar sun farka da matsanancin hayaki da ya turnuke yankin, wanda aka ce na wani minista ne.
Ko da yake ba a san musabbabin tashin gobarar ba, Amma rahotanni sun nuna cewa, gobarar ta shafe sama da sa’o’i biyu, ba tare da Kawo dauki ko kadan daga hukumar kashe gobara ta jihar ba.
Gidan Man yana kusa da wasu gine-ginen kusa da titin Aba kuma ƴan mitoci kaɗan daga tsakiyar birnin.
Daga bisani dai, An ga mazauna yankin da dama dauke da ruwa yayin da suke tallafawa kokarin da ma’aikatan kashe gobara ke yi na dakile gobarar