Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a jiya ta ce ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da laifin damfarar jama’ar jihar a wani shiri na Ponzi.
Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Ishola Babaita, ne ya yi wa manema labarai jawabi hakan a hedikwatar rundunar, inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne ta hanyar dabarun aikin ‘yan sanda a cikin al’umma.
Ya ce mutanen shida da ake zargin sun hada da ‘yan Najeriya biyu, Abdullahi Yusuf Adamu, mai shekaru 26, dan yankin Jekadafari da ke jihar da Jasper Jacob mai shekaru 33 daga jihar Taraba da kuma Dafton Wakon Elysee, da Hopko Adolphe, da Jamal Salami, da Emmanuel Haunukon dukkansu ‘yan asalin kasar Jamhuriyar Benin.
A cewarsa, ‘yan asalin jamhuriyar Benin hudu da ake zargin sun shiga jihar ba bisa ka’ida ba tare da wasu mutane 109 a ranar 18 ga watan Janairu.
Babaita ya bayyana cewa, wadannan matasa 6 su ne suka dauki matasa Dauyin mutane 109 a jihar domin ne momusu abokan hulda, inda ya ce bisa binciken da suka yi, an gano cewa wadanda ake zargin sun shiga cikin shirin Ponzi ne domin damfarar jama’a da ba su ji ba gani.
Ya kara da cewa, a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun shiga wata sana’ar sada zumunta ce ta yanar gizo mai suna QNET.
Sai dai wasu daga cikin wadanda ake zargin da suka zanta da manema labarai sun musanta zargin da ake yi musu, inda suka ce sana’ar ta su, wacce akeyi ta yanar gizo ce ta gaskiya ce. Sun ce a shirye suke su kare kansu a kotu.