By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Atakumosa ta gabas ta tsakiya a jihar Osun, Gbenga Ogbara.
An tattaro cewa an harbe Ogbara a gidansa da ke Ogangan, da sanyin safiyar Litinin.
DUBA WANNAN LABARIN: Hukumar NDLEA Ta Kama Kunshin 101 Na Hodar Iblis A Filin Jirgin Saman Jihar Legas
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma ta yi alkawarin cewa wadanda suka aikata laifin ba za su tafi ba tare da an hukunta su ba.
Opalola ya ce: “Wasu ‘yan bindiga ne suka kashe Shugaban APC da misalin karfe 12 na safe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa biyo bayan faruwar lamarin ya sanya shakku da zaman dardar ga mazauna yanki.
Tuni dai aka tura jami’an tsaron ‘yan sanda zuwa yankin dan ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin wadanda suka aikata laifin inda tace ba za su tsere wa shari’a ba.”