Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yabawa ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami SAN bisa raba sama da buhu dubu goma sha shida na hatsi iri-iri a matsayin tallafi ga al’ummar jihar a cikin watan Ramadan.
Bagudu ya ce gwamnatin jihar Kebbi ta kuma sayo buhunan hatsi iri-iri da suka kai kimanin buhu dubu talatin da biyar domin rabawa al’umma a dukkanin kananan hukumomi ashirin da daya na jihar.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ne ya bayyana haka a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi a ranar Asabar a wajen rabon kayan abinci ga mutanen da Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN ya bayar.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Babale Umar Yauri ya bukaci masu hannu da shuni da masu rike da madafun iko da kuma zababbun shugabanni da su ci gaba da tallafawa marasa galihu a cikin al’umma a koda yaushe.
A nasa jawabin Abubakar Malami SAN, ya bayyana cewa an yi hakan ne da nufin kawo agaji ga al’umma da kuma inganta rayuwarsu musamman a wannan wata na Ramadan da ke nuni da jinkai. don samun babban riba.
Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki wajen rabon kayayyakin da su ji tsoron Allah ta hanyar tabbatar da cewa kayayyakin da aka bayar sun kai ga wadanda aka zayyana, yayin da ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kara zage damtse da addu’o’in neman taimakon Allah a cikin wannan wata na Ramadan domin magance kalubalen zamantakewa, tattalin arziki da tsaro da ke addabar al’umma najeriya.
Sai dai Ministan ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma jam’iyyar APC mai mulki bisa kokarin kyautata rayuwar talakawa ta hanyar shirye-shiryen tallafi daban-daban da kuma tsare-tsare.
Taron ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Sa’idu Nasamu Dakingari, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi, Alhaji Hassan Mohammed Salla, shugaban kungiyar NUT na kasa, Alhaji Nasiru Idris (Kauran Gwandu), mai taimakawa Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Faruk Musa (Enabo) da Malamai, da Sarakunan gargajiya da dai sauran su.