By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyar ne aka yi garkuwa dasu a garin Tegina dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Idan dai za’a iya tunawa jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiyya dake Tegina a farkon wannan shekarar.
Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa a karshen makon nan ne ‘yan bindigar suka koma unguwar suka yi awon gaba da ma’aikatan masana’antar su biyar. ‘Yan bindigar dai sun kai kimanin su 10, inda aka ce suna dauke da manyan bindigu na AK47.
Majiyar tace sun mamaye garin ne da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar inda suka je wani kamfanin samar da ruwan leda dake daura da makarantar sakandare ta ‘yan mata ta gwamnati dake cikin al’ummar.
“Sun kawo mana hari ba tare da sani ba saboda sun zo da ƙafa. Mun fara jin karar harbe-harbe kuma muka gudu domin tsira da rayukanmu. Sun je ma’aikatar ruwa ta leda inda aka tafi da mutane biyar,” in ji daya daga cikin majiyoyin.
Sai dai da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace yana cikin wani taron ganawa.
Kazalika yace “Ya yi alkawari zai mayar da martani daga baya amma ya gaza yin hakan har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.