• Hadarin ya raunata mutum da dama Amma Direban Motar ya rayu.
• Motoci biyun ne sukayi taho mugama da juna ya yin da Direban daya daga ciki ke gudun wuce kina.
• Shugaban hukumar kiyaye haddura reshen shiyar ya tabbatar da afkuwar lamarin.
A kalla mutum goma ne suka rasa rayu kan su a daran jiya juma’a, sanadiyayyar mummunan hadarin mota daya afku a yankin Kanbi na karamar hukumar Moro na jihar Kwara.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa, wata farar motar kabu-kabu Kirar Toyota, mai dauke da lamba XC15SMK, ta yi taho mugama da wata babban mota kirar Ford.
Kana rahotanni sun nuna cewa, Mutum goma sha tare ne hadarin ya rutsa da su, ya yin da Mutum goma suka mutu nan take.
Wauran da suka sami mummunan raunika an kaisu asibiti domin duba lafiyar su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kama abduljabbar
Kazalika rahotannin sun nuna cewa, an adana kawarwakin wadanda su ka mutu, a asibitin Horaswa na jami’ar Ilorin wato UITH.
Wani shaidar gani da Ido ya bayyana cewa, “Direban Motar kabu-kabu na gudun wuce sa’a ne, ya yin da mutar ta kwace mashi, kuma ya afka wa bababr motar.” Inji shi.
Lokacin da aka tuntubi babba Kwamandan na hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen shiyar Jonathan Owoade, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya ce, “Matukin motar da ke dauke da Fasinjoji goma sha takwas, ya tsira da rayuwar shi.” Kamar yadda ya bayyana.
“Sun taho daga garin Minna ne zasu tafi Offa ya yin da lamarin ya afku.” Inji shi.
” Mutum goma sun mutu nan take, inda wadanda suka rayu da suka hada da matukin motar, an kai su asibiti domin duba lafiyar su” a cewar shi.
A karshe ya ce, ” An kai gawar-wakin wadanda suka mutu, zuwa asibitin horaswa na jami’ar UITH” inji Shugaban hukumar ta kiyaye haddura.