Da duminsa: Shugaban jam’iyyar PDP na Ondo ya rasu
Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu.
Rahotanni sun ce shugaban jam’iyyar ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tabarbarewar Tattalin Arziki: Ka magance al’amura kafin ya fi ƙarfin ku – Gwamnonin PDP
Mista Kennedy Peretei, Sakataren Yada Labarai na PDP na Ondo, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Laraba.
Ya ce nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta yi magana da manema labarai a hukumance kan lamarin
A wani labarin kuma:Oshiomhole ya yarda cewa Buhari ya gaza, yanzu ba jarumin su bane ba – Aisha Yesufu
Wata mai sharhi kan al’umma, Aisha Yesufu, ta ce Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole ya amince cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza.
Yesufu tace Oshiomhole ya baiwa ‘yan Najeriya izinin sukar Buhari.