Oshiomhole ya yarda cewa Buhari ya gaza, yanzu ba jarumin su bane ba – Aisha Yesufu
Wata mai sharhi kan al’umma, Aisha Yesufu, ta ce Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole ya amince cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza.
Yesufu tace Oshiomhole ya baiwa ‘yan Najeriya izinin sukar Buhari.
KARANTA WANNAN LABARIN:An sanya wa ƴan Najeriya igiyar zato kan dukiyar ƙasa, amma matalauciya ce – Onanuga
Ta na mayar da martani ne ga kalaman Oshiomhole na cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala saboda munanan manufofin tattalin arziki na Buhari.
Ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai iya daukar alhakin wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki ba.
Da yake aikawa a kan shafin sa na X, Yesufu ta rubuta: “A yanzu Adams Oshiomhole ya yarda cewa Buhari ya gaza kuma ya ba ‘yan kasa ‘izni’ su soke shi.
“A jiya Buhari ne gwarzonsu. Sun kare shi kuma kullum suna Daura. Yau sun zarge shi.
“Sabon gwarzon su shine mutumin Legas. Sai dai a jira mulkin da aka samu ba bisa ka’ida ya kare ba sai bakinsu ya bude.
“Abin da ya dauka kawai Buhari ya bar ofis kuma biyayya ta koma ga wanda ke zaune ba bisa ka’ida ba.
“A yanzu Adams Oshiomhole ya ba ku dama ku soki Buhari
A wani labarin kuma:Tabarbarewar Tattalin Arziki: Ka magance al’amura kafin ya fi ƙarfin ku – Gwamnonin PDP
A yayin da ake fama da wahalhalu a kasar, gwamnoni a karkashin jam’iyyar PDP, sun yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar All Progressives Congress da ta tashi tsaye wajen magance lamarin kafin ya fita daga kangin.
Gwamnonin sun ce wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ya biyo bayan kalubalen tattalin arziki da tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta.