Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya tabbatarwa da mutanen jihar Yobe zai dawo da zaman lafiya a jihar idan aka zaɓe shi.
Atiku ya kuma yi alƙwarin buɗe iyakokin dake tsakanin Nijar da Yobe domin samar da hanyar wucewar mutane da kayan amfanin gona. Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Jaruma Maryam Wazeeri, Laila ta shirin Labarina ta samu ƙaruwa
Da yake magan a wajen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Atiku yace idan aka zaɓe shi zai samar kuɗi domin mata da matasa su kama sana’o’i.
A kalamansa:
“Idan kuka zaɓi PDP, zaman lafiya zai dawo a Yobe. Zamu tabbatar da cewa mun buɗe makarantun mu, ta yadda ƴaƴan mu za su cigaba da zuwa makaranta.”
“Mun kuma yi alƙawarin zamu samar da jari ga matasa da mata ta yadda zasu fara kasuwancin su, domin samun damar yin rayuwa mai inganci.”
“Mun yi alƙawarin sake buɗe iyakokin ƙasar nan ta yadda kasuwancin dake tsakanin mu da makwabtan mu zai bunƙasa yadda ya dace.”
EFCC Ta Tura Wani Babban Sanata Gidan Gyaran Hali Bisa Almundahanar Kuɗi
A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC ta tasa ƙeyar wani sanata gidan gyaran hali, bayan ya daɗe da boyewa saboda tsoron hukunci.
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta bayyana cewa tayi caraf da sanatan dake wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Peter Nwaoboshi.
A kwanakin baya ne dai wata kotun ɗaukaka ƙara a jihar Legas ta yankewa sanatan hukuncin shekara bakwai a gidan gyaran hali bisa cin kuɗin haram.