Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce idan har tsarin ‘yan sanda ya yi tasiri a Najeriya, rabin wadanda ke gwamnatin Buhari, za su kasance a gidan yari.
Ya bayyana haka ne a wani taro na biyu na yan takarar shugaban kasa da gidan talabijin na ARISE tare da hadin gwiwar Cibiyar Dimokaradiyya da Ci Gabanta (CDD) suka shirya.
KARANTA ANAN: Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Makwanni 2 A Burtaniya
Adebayo ya ce, “Kada mu gudu daga kafa gwamnati amatakin tarayya, akwai kundin tsarin mulki na taimakawa da zan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu.
A cikin kundin tsarin mulkin, yana da duk abin da ake bukata don kawar da laifuka.
“Kuma matakai biyu da za a bi don kawar da miyagun laifuka shi ne kawar da laifuka a cikin gwamnati, wannan shine abu mafi wahala a Najeriya.”
“Daya daga cikin dalilan da ya sa ba mu da ingantaccen tsarin ‘yan sanda shi ne, idan muna da ingantaccen tsarin ‘yan sanda, rabin wadanda ke gwamnati za su kasance a gidan yari.”
A karo na biyu na zauren taron akwai ‘yan takarar shugaban kasa hudu da suka halarta – Omoyele Sowore, na AAC. da Mallam Yabagi Sani, Farfesa Peter Umeadi, da Adebayo.
Taro na farko ya hada ‘yan takarar shugaban kasa guda hudu da aka zabo bisa la’akari da ayyukan jam’iyyunsu a wani bincike da CDD ta gudanar a yanar gizo.
Manyan jam’iyyun sun hada da Labour Party (LP), (APC), (PDP) (NNPP).
A wani labarin kuma: Malaman ASUU Zasu Gudanar Da Zanga Zanga Kan Rage Musu Albashi
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta shirya gudanar da zanga-zangar kwana guda a fadin kasar nan.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ASUU za ta yi zanga zangar ne domin nuna rashin amincewa da yadda Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da shirin “ba aiki, babu biya” ga malaman jami’o’in kasar nan.
Za a gudanar da zanga-zangar ne a matakan reshen kungiyar da ke fadin cibiyoyin jami’o’in gwamnati a fadin kasar, kuma za a yi ta ne a matsayin rana ta kyauta ga dukkan malaman da suke mambobi.