Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, bayan ziyatar kasar Birtaniya don duba lafiyar sa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Buhari ya dawo Najeriya ne, bayan shafe makwanni biyu a Burtaniya.
KARANTA ANAN: Malaman ASUU Zasu Gudanar Da Zanga Zanga Kan Rage Musu Albashi
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Garba Shehu Ya ce Buhari ya sauka a filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 7:22 na daren Lahadin nan cikin koshin lafiya.
Yayin ziyarar duba lafiyar sa a Birtaniya, Buhari yayi amfani da damar, wajen ziyartar sabon sarkin Ingila, Sarki Charles III.
- A wani labarin kuma: Dubban Magoya Bayan Jam’iyyun APC, Da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Taraba
Karshen mako nan ya kasance lokaci mafi muni ga jam’iyyar APC, da Labour Party, LP a jihar Taraba ba, yayin da dubban magoya bayanta suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a shiyyar Kudu maso Kudu.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa guguwar sauyin shekar ta kuma shafi sauran jam’iyyun siyasa, da ke da zama a kananan hukumomi biyar na Taraba ta Kudu.
Masu sauya shekar sun kai 11,000 a ranar Asabar din da ta gabata a wurin yakin neman zaben Sanata mai ci, Darius Ishaku a Wukari.
Comments 2