By Abbas Yakubu Yaura
A yammacin ranar Lahadi ne mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ya yi murabus daga mukamin kwamishinan noma da albarkatun kasa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gawuna, Hassan Fagge, ya fitar, ta ce mataimakin gwamnan ya yi murabus a matsayin kwamishina domin ci gaban harkokin siyasar sa.
“Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ni karfi da hikima tare da yi mani jagora wajen tafiyar da ma’aikatar noma da albarkatun kasa tsawon shekaru bakwai a karkashin Mai Girma Gwamnan kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje.
“A cikin wadannan shekarun, na yi aiki a matsayin kwamishinan noma a karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Ganduje, na samu ilimi da dama, na fadada hangen nesa na, na kuma samu gogewa a hidimar jama’a.
“A waɗancan shekarun, mun yi aiki tare da hangen nesa kuma mun sami nasarori da yawa a fannin noma.
“Na yaba da damar da aka ba ni na zama kwamishina a karkashin gwamnatin Ganduje wadda a yau ta sa na kasance cikin manyan kwamishinonin noma na kasar nan.
“Shawarar da na yi na yin murabus daga mukamin kwamishinan noma da albarkatun kasa shi ne in ci gaba da harkokina na siyasa. Zan ci gaba da bayar da gudunmawar ci gaban jihar a matsayina na mataimakinka mai aminci a kan aikin da mutanen Kano suka ba mu,” Mista Gawuna ya kara da cewa.
Kawo yanzu dai kwamishinoni da dama ne a jihar Kano suka ajiye mukaman su dan tsayawa takara tun bayan sanarwar da gwamna Ganduje ya bayar na cewa kofa abude take ga mai bukatar tsayawa takara zai iya sauka daga mukamin sa.
Comments 1