Wata mata ta koka kan yadda ƙawarta tayi mata ƙwacen saurayi bayan ta haɗa su.
Matar mai suna Munira ta sanya wasu bidiyoyi waɗanda suka nuna irin kusancin dake tsakanin su da ƙawarta wacce tayi mata cin amana. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: 2023: Tsohuwar Ƴar Takarar shugaban kasa na SDP ta koma APC, ta amince da Tinubu
Ta kuma nuna lokacin da ta haɗa saurayin nata da ƙawar mai suna Adeola Ariyo.
Adeola taje wajen taron murnar samun juna biyu na Munira lokacin da ita da saurayin ta ke murnar sun kusa zama iyaye.
Munira ta kuma nuna yadda a lokuta da dama suke tafiya tare da Adeola idan ita da saurayinta za su ɗan fita shaƙatawa.
Yanzu dai Adeola ta koma soyayya da saurayin Munira wanda shine mahaifin abinda zata haifa.
Wannan cin dundunniyar da Adeola ta yiwa Munira yayi mata zafi sosai, inda take cewa wasu lokutan kana tare da maƙiyin ka ne baka sani ba.
Cin amana dai wani abu ne mai matuƙar sosa zuciya, ya kuma fi zafi da raɗaɗi idan wanda yayi cin amanar na kusa da mutum ne.
Ƙwacen saurayi dai da ƙwacen budurwa wani sabon abu ne da yake ƙoƙarin zama ruwan dare a wannan zamanin.
Magidanci Na Son Auren Mace Ta Biyu, Zai Biya Sadakin N500k, Ya Bayyana Sharuɗɗan Sa
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci na neman matar da zai yi wuff da ita, ya bayyana sharuɗɗan sa.
Wani magidanci mai shekara 57 a duniya wanda ya fito daga jihar Kaduna yana neman ƙara aure inda zai auri mace ta biyu.
Shafin haɗa aure na Halal matchmaking a Twitter shine ya bayyana abubuwan da magidanci yake buƙata a wajen duk wacce ta shirya zata aure shi.