Labarin dake shigowa Jaridar Dimokuradiyya na nuni da cewa; cikin wasu kalaman gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta janye dukkannin takunkuman da ta sanya Turkiya matukar kasar ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da ta bai wa mayakan Kurdawa damar ficewa daga yankinsu zuwa tudun mun tsira.
Babu wani cikakken bayani ko Turkiyyar ya zuwa hada rahoton nan za ta tsagaita wuta.