Tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta isa ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Ministar ta yi aiki a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta rike ofishin Ministar Jin Kai Da Kawar Da Fatara Da Bala’i tsawon shekaru 4.
Karanta nanDa dumi-dumi: Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan zaɓen Ebonyi
Ana tuhumar ta ne kan babakere da kudi har N37,170,855,753.44 da ake zargin wani dan kwangila mai suna James Okwete ya karkatar ta hannunta.
Ta rubuta a shafukan sada zumunta a safiyar ranar Litinin cewa, “A bisa ga umarnina, na isa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) don karrama goron gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi mani na bayar da karin haske kan wasu batutuwan da hukumar ke bincike.
A wani labarin kumaJami’ar Tafawa Balewa Dake Bauchi Ta Karyata Batun Aiki Da Farfesan Bogi
Hukumar gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta bayyana a matsayin labarin karya da tatsuniyoyi kawai da Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) ta bayyana cewa ta bankado malaman bogi kusan 100 a wasu jami’o’in Najeriya.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Zailani Bappah ya raba wa manema labarai a jiya, ya ce labarin na tatsuniyar almara ce kawai, wani shiri ne na kirkire-kirkire kuma wani yunkuri ne na bata sunan jami’ar da aka yi ta fama da shi.
A cewar sanarwar, labarin ya nuna cewa a cikin 100 da ake zargin malaman jami’ar akwai sunayen mutane bakwai a matsayin ma’aikatan jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi