Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga Malam Mele Kyari, babban jami’in gudanarwa na rukunin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), a yayin bikin cikarsa shekaru 59 da haihuwa a ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya yabawa Mele Kyari akan kwazonsa da kwarewarsa, inda ya amince da shi a matsayin daya daga cikin manyan jami’an gudanarwa mafi dadewa a tarihin kamfanin makamashi mafi daraja a Afirka.
Karanta nanDa dumi-dumi: Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan zaɓen Ebonyi
Mele mutum ne mai aiki fiye da kalmomi yana tunkarar ayyuka a hankali da kuma ikonsa na gano matsaloli masu sarkakiya da samar da hanyoyin da za a bi a hankali hakn ya ba shi damar ci gaba da yi wa al’ummarmu hidima mai kima in ji Shugaban.
Shugaban ya gabatar da addu’o’in samun tsawon rai ga Kyari inda ya bayyana fatan Allah ya karawa shugabannin ‘yan kasuwa hikima da karfin gwiwa a kan hidimar da yake yi wa Nijeriya.
A wani labarin kumaDaga Karshe Tsohuwar Minista Sadiya Umar Faruk Ta Ziyarci Hukumar EFCC
Tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta isa ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Ministar ta yi aiki a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ana tuhumar ta ne kan sama.da fadi da wasu kudi har N37,170,855,753.44 da ake zargin wani dan kwangila mai suna James Okwete ya karkatar ta hannunta.
Ta rubuta a shafukan sada zumunta a safiyar ranar Litinin cewa “A bisa ga umarnina, na isa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) domin karrama goron gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi mani na yin karin haske dangane da wasu batutuwa da suka shafi cin hanci da rashawa da hukumar ke bincike.