Mazauna unguwar Aponrin a Agbowo cikin birnin Ibadan a jihar Oyo, sun koka kan rashin wayoyin salular su bayan wani aikin bauta da wani fasto mai suna Owen Abraham ya shirya.
A cewar rahoton jaridar Legit.ng, sama da wayoyi. Android da iPhone 52 ne na waɗanda suka je wajen bautar na kwana biyar fasto Abraham yayi awon gaba da su.
KU KARANTA KUMA: Darajar Naira Ta Faɗi Da Kaso 10% – Inji Bankin Duniya
Wasu daga cikin waɗanda abin ya ritsa da su sun bayyana cewa faston ya gaya musu cewa ubangiji ne ya turo shi daga Gambia zuwa Ibadan domin ya shirya aikin bautar.
Sun bayyana cewa faston yace anyo masa wahayi ne ya gaya musu cewa su bayar da wayoyin su da sauran kayayyakin su, waɗanda daga baya ya ranta ana kare da su.
Mrs Grace Akintola, wata wacce abin ya ritsa da ita, ta bayyana cewa:
“Wani ɗan unguwar mu ne ya gayyace ni ziwa wajen. Mai gudanar da aikin bautar ya sanya kayan fasto, yace zai siyawa ɗaya daga cikin mu gida. Yace gidan an gama ƙawata shi.”
“Ya yiwa wasu mutanen da suka je wajen alƙwarin zai basu kuɗi, ko ƴan siyasa ba zasu iya bayar da kuɗin da yayi alƙawari ba.”
“A ranar ƙarshe, ya siyar da robar ruwa kan kuɗi N4,800. Yace akwai turare a cikin ruwan, mutane da yawa sun biya kuɗin ruwan.”
A halin da ake ciki, ƴan sanda sun bazama neman wannan faston domin kamo shi.
Tabdijam: Yadda Uba Ya Gwada Diyarsa Domin Gano Ko Tana Sana’ar Gidan Magajiya a Makaranta
Wani magidanci ɗan Najeriya ya gwangwaje ɗiyar sa da kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan yayi mata gwajin kwantawa da wani saboda N300k.
Da yake magana da Shuga Plum, wani mai ɗaukar bidiyo, mutumin yace yana ganin maza ke ɗaukar ƴanmata sannan yana son ya san halayyar ɗiyar sa a makaranta.