Sojoji sun lalata Ma’aikatar makaman kungiyar ISWAP tare da kashe mayakanta akalla 100, ciki har manyan kwamandojinta a tsakiyar watan Ramadan din da muke ciki.
Manyan kwamandojojin kungiyar 10 tare da sauran mayakan sun sheka lahira ne bayan dakarun Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Tafkin Chadi (MNJTF) sun yi musu dirar mikiya, inda suka yi raga-raga da masana’antar makaman da ke Arina Woje, a yankin Tafkin Chadi.
Kakakin rundunar MNJTF, Kanar Muhammad Dole ya bayyana cewa, “Kwamandojin kungiyar da sojoji suka kashe sun hada da Abubakar Dan Buduma, Abubakar Shuwa, Abu Ali da Abu Jubrilla da sauransu.
Sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ta ce sojojin sun yi wa mafakar mayakan na ISWAP da ke Zanari da Fedondiya da sauran wurare raga-raga ne ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma dakarun sojin kasa.
A wani labari Kuma na daban.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a majalisar tarayya, Shina Peller, ya yi kira ga matasa da sauran ‘yan Najeriya da su yi hattara da ‘yan siyasar da za su yi amfani da su wajen cika burinsu na siyasa a kasar.
Dan majalisar daga jihar Oyo ya bayyana haka ne a sakonsa na Easter da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kola Popoola ya rabawa wakilinmu ranar Litinin.
Ya bayyana Yesu Kiristi a matsayin mutum ne wanda koyarwarsa da kyawawan halayensa ke wakiltar zaman lafiya da kowace al’umma har da Najeriya ke bukatar ci gaba.
Dan majalisar tarayya ya lissafa dabi’un Yesu Kiristi da suka hada da zaman lafiya, tawali’u, juriya, sadaka, hakuri, gaskiya, jajircewa, tausayi, karimci, aminci, amana, adalci, kamun kai, gafara, kauna da mutunta wasu, wadanda ya ce duka su ne halayen da ake buƙata don al’umma don samun ci gaba.
Ya hori Kiristoci da Musulmai da su yi koyi da kyawawan halaye na Kristi don samun damar magance mafi yawan matsalolin da kasar ke fuskanta.
Ya ce, “Don haka yayin da muke gudanar da bukukuwan Easter, ina rokon mu duka mu yada soyayya, wa’azin zaman lafiya da watsar da alheri da jin dadi a ko’ina a kewayen mu.
“Mu kasance masu hakuri da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabilanci da siyasa ba. Sama da duka, mu kasance masu adalci a cikin maganganunmu da mu’amalarmu da juna.
“Abu mai mahimmanci, kamar yadda babban zaben 2023 ya nuna, ba za mu bar wani dan siyasa ya yi amfani da mu ba da gangan ko kuma ya yi amfani da mu wajen cika burinsa na siyasa ko sha’awarsa wajen cutar da muradun kasarmu baki daya.
“Kada mu yarda a yi amfani da kanmu a matsayin kayan aikin rarrabuwa da tashin hankali. Lokaci ya yi da zamu yi watsi da ubangida na siyasa amma mu mai da hankali kan gina cibiyoyi masu ƙarfi waɗanda tsara waɗanda ba a haifa ba za su yi alfahari da su. Har yanzu, Barka da Easter zuwa gare mu duka.”