Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Legas ta rufe makarantar Chrisland har sai abinda hali yayi bisa zargin aikata fyade.
Wata dalibar makarantar ‘yar shekara 10, an ce abokan karatunta sun yi mata fyade a lokacin da tayi tafi zuwa kasar Dubai.
Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda da dama ke kira ga gwamnati da ta dauki mataki kan lamarin.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa (MDAs) na binciken zargin cin zarafin dalibar makarantar Chrisland da suka hada da ma’aikatar ilimi; Ofishin Tabbatar da ingancin Ilimi; Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Al’umma; Ma’aikatar Shari’a da dai sauran hukumomi.
Sanarwar da kungiyar ta MDAs ta sanya wa hannu, ta bayyana cewa an kai karar zargin aikata laifin zuwa ga kwamishinan ‘yan sanda.
“Saboda zarge-zargen, mun himmatu wajen tabbatar da cewa an samar da isassun tallafin kayan jinya da na psyho-sosula. Hakan na nufin tabbatarwa da jama’a aniyar Gwamnatin Jiha ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da kare yara, musamman wajen tabbatar da cewa duk cibiyoyin da suka shafi yara a jihar, su tsara da aiwatar da tsare-tsaren da suka dace da Dokar Zartaswa (No.EO/) AA08 ta shekarar 2016), Shirin Kare Yara na Jihar Legas.”
Don haka gwamnatin jihar tana tunatar da jama’a cewa duk wanda ya aikata wani abin da ya faru na lalata da yaro ya aikata laifi kuma yana da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 14. “Wannan ya haɗa da samarwa, rarrabawa, karɓa, ko mallakar hoton batsa na kananan yara.”
Tun da farko dai Jaridar Daily Trust ta tuntubi makarantar domin jin ta bakinta game da lamarin.
Wani wakilin makarantar wanda ya yi magana ta wayar tarho ya ce, “Eh, wannan makarantar Chrisland ce. Ba a ba ni izinin yin magana kan batun ba. Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sanarwa a hukumance. Na gode.”