Dakarun sojoji na bataliyar 21 task force brigade, Operation Hadin Kai, tare da haɗin guiwar ƴan sakai (CJTF), sun halaka mayakan Boko Haram da dama a Borno.
Zagazola Makama, wani masanin lamuran tsaro wanda ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya rahoto cewa ƴan ta’adda sun sheƙa barzahu ne bayan sojoji sun kai wani sumame a sansanin su guda shida ranar Asabar. Rahoton The Cable
KU KARANTA KUMA: Anya kuwa: Bidiyon sauyin da wani matashi ya samu ya sanya mutane rudani
Wata majiya ta gayawa Zagazola Makama cewa dakarun sojojin sun tarwatsa maɓoyar ƴan ta’addan a Bula Agaida, Bula Yaga, Bula Lambai, Kuluri, Bula Umar, da sabuwar Churchur a ƙaramar hukumar Bama ta jihar.
Sojojin kuma sun ƙwato wata mota a hannun ƴan ta’addan a yayin sumamen.
“Dakarun sojojin sun gano wani babban sansanin ƴan ta’addan a Bula Agaida da Bula Yaga. Sojojin sun gano wata kasuwar ƴan ta’adda sannan suka lalata ta.” A cewar majiyar.
“Majiyar ta kuma tabbatar da cewa da yawa daga cikin ƴan ta’addan sun gudu sun bar sansanin su yayin da sojojin suka lalata waɗanda aka sake ginawa.”
Ɓata Gari Sun Lalata Sakatariyar Wata Babbar Hukuma a Jihar Zamfara
A wani labarin na daban kuma, wasu ɓata gari sun lalata sakatariyar wata babbar hukumar a jihar Zamfara.
Ɓata gari sun lalata sakatariyar hukumar yaƙi da dabanci ta jihar Zamfara.
Kwamandan hukumar Bello Bakyasuwa, ya bayyana cewa an farmaki sakatariyar ne bayan an sanar da sakamakom zaɓen gwamnan jihar a ranar 21 ga watan Maris 2023.