Daliban Jami’ar Tarayya ta Lokoja (FUL) a ranar Litinin din nan sun roki kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da kar ta koma yajin aikin sai bayan kammala jarrabawar zangon karatu na biyu.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayyana cewa Koke-koken daliban ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar ASUU ta ke gudanar da taron Majalisar a ranar Litinin din nan inda ake tattaunawa kan gazawar gwamnatin tarayya na gaza biyan albashin mambobinta bayan ta koma bakin aiki a ranar 14 ga watan Oktoba daga yajin aikin da ta yi na watanni 8.
Wani sashe na daliban, wadanda suka yi wannan roko a lokacin da suke zantawa da kamfanin dillacin labarai na Kasa NAN a Lokoja, sun ce zai zama bala’i idan ba a gudanar da jarrabawarsu ta ranar 14 ga watan Nuwamba ba.
KU KARANTA KUMA ASUU Zata Gudanar Da Taro Kan Zaftare Musu Rabin Albashi
Miss Joy Abuh, dalibar Kimiyyar Siyasa, ta ce rokonta shi ne kada taron ASUU na ranar Litinin ya kare da komawa yajin aikin da aka dakatar.
“Mun zauna ne bayan dakatar da yajin aikin da muka yi da gaske kuma mun shirya jarabawar zangon karatu na biyu da za a fara ranar Litinin mai zuwa.
“Zai yi mana babu dadi a FUL idan ba za a yi jarrabawar ba kamar yadda aka tsara, duba da yadda muka yi asarar watanni takwas a gida.
“Rokon ta musamman shi ne kar kungiyar ta ayyana duk wani yajin aiki a karshen taron da suka yi yau a Abuja,” inji ta.
Wata daliba mai suna Adeiza Ibrahim dake sashin ilimi ta koka kan illar duk wani yajin aikin da daliban Najeriya ke fuskanta tare da yin kira da a sake tunani daga ASUU domin a ci gaba da gudanar da harkokin ilimi yayin da suke sasanta rikicin da ke tsakanin su da gwamnati.
“Ina ganin an tafka barna sosai ga tsarin ilimi na kasa don haka ya kamata a yi la’akari da yadda za a bi da sabon shiri domin muna magana ne kan makomarmu, matasan kasar nan.
“Idan a karshen, ba za a bar mu mu rubuta wannan jarrabawar ta zangon na biyu ba, to zai yi muni da matsala,” in ji Ibrahim.
A Wani Labarin Kuma Akalla Mutane Sama Da Miliyan Daya Ambaliyar Ruwa Ta Shafa – Hukumar Agaji
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Bayelsa (BYSEMA), ta ce ambaliyar ruwa ta shafi mutane akalla miliyan 1.3.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayyana cewa, Hakan ya fito ne a ranar Litinin din nan ta hanyar BYSEMA a Yenogoa wanda aka rabawa manema labarai.