Akalla dalibai ‘yan mata 42,954 ne suka bar makaranta tsakanin watan Yulin shekarar 2021 da Yuni shekarar 2022 bayan sun sami juna biyu.
Wannan na zuwa ne a cewar sabon rahoton da babban mai binciken kudi na kasar Tanzaniya ya fitar ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa’adin Ranar Kammala Biyan Kudin Aikin Hajjin Bana Ga Maniyyatan Kaduna
Rahoton CAG na shekarar 2021 zuwa 2022 da aka gabatar a majalisar dokokin kasar a Dodoma babban birnin kasar, ya ce daga cikin ‘yan mata 42,954 da ke da ciki, 23,009 sun fito daga makarantun sakandare, a yayin da 19,945 kuma suka fito daga makarantun firamare.
Rahoton ya ce ‘yan matan da ke makarantun sakandire masu ciki sun kai kashi 28 cikin 100 na ‘yan mata 82,236 da aka tsara za su kammala karatunsu na matakin farko a shekarar 2021.
Rahoton ya ce ‘yan matan da aka yi wa ciki sun fito ne daga kananan hukumomi 19 na kasar nan.
Rahoton ya ce makarantun sakandaren da suka fi yawan ‘yan mata masu ciki a karamar hukumar Kinondoni da ke yankin Dar es Salaam da ke da ‘yan mata 4,652.
Rahoton ya kara da cewa majalisar gundumar Newala da ke yankin Mtwara ta biyo baya da ‘yan mata 3,783 da kuma karamar hukumar Misungwi da ke yankin Mwanza mai ‘yan mata 2,570.
A bangaren makarantun firamare kuwa karamar hukumar Kwimba da ke yankin Mwanza ce ta fi kowacce yawan ‘yan mata masu ciki a tsawon lokacin da ake bitarsu tare da ‘yan mata 9,045, sai kuma karamar hukumar Uvinza da ke yankin Kigoma da ke da ‘yan mata 2,172, inji rahoton.NAN.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Na Binciken Jami’an Da Suka Ci Zarafin Wani Mutum A Faifan Bidiyo
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta fara gudanar da bincike kan yadda ‘yan sanda suka ci zarafin wa wani mutum a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wani faifan bidiyo ya bazu a shafukan sada zumunta a garin Fatakwal, inda aka kama wani dan sanda dauke da makamai yana cin zarafin wani mutum a gaban matarsa a jihar Ribas.