Shigo da babura da aka fi sani da Okada a Najeriya ya ragu zuwa Naira biliyan 212.64 a shekarar 2022 wanda ya nuna an samu raguwar kashi 42 cikin 100 daga Naira biliyan 367.39 da aka kashe a shekarar 2021.
Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na kididdigar cinikayyar kayayyaki ta kasashen waje wanda kuma ya nuna cewa lissafin shigo da babura ya fadi da kashi 22 cikin 100 zuwa Naira biliyan 46.43 a rubu’i na hudu na shekarar 2022 (Q4’22). daga Naira biliyan 59.63 a Q3’22.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalibai ‘Yan Mata 42,954 Basa Zuwa Makaranta Saboda Juna Biyu A Tanzania – Rahoto
An samu koma baya ne a Q3’22 yayin da kudin shigo da babura ya karu da kashi 86 zuwa Naira biliyan 59.63 sannan ya ragu da kashi 22 cikin dari zuwa Naira biliyan 46.43 a Q4’22.
PUNCH ta lura cewa wannan faduwar na iya kasancewa sakamakon dokar hana Okada a wasu jihohin kasar nan, musamman jihar Legas da ta fi kowacce yawan shigo da shi.
Idan za a iya tunawa, a watan Mayun 2022 ne gwamnatin jihar Legas ta haramta gudanar da ayyukan babura na kasuwanci a kananan hukumomin jihar guda shida da suka hada da Ikeja, Surulere, Eti-Osa, Lagos mainland, Lagos Island da Apapa, daga bisani kuma ta tsawaita dokar zuwa wasu hudu kananan hukumomi Kosofe, Oshodi-Isolo, Shomolu da Mushin.
Gwamnati ta sanar da cewa haramcin ba shi da iyaka kuma duka.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an kama babura sama da 2000 na mahaya a ranar da aka ba su izinin dakatarwar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Gbenga Omotoso, ya bayyana cewa kimanin babura 5,000 a baya an murkushe su a Q1 22.
A wani labarin kuma, Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa’adin Ranar Biyan Kudin Aikin Hajjin Bana Ga Maniyyatan Kaduna
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kaduna ta baiwa maniyyata fiye da 2,000 a jihar wa’adin kwanaki 10 da su kammala biyan Naira miliyan 2.919 na kujerun aikin Hajjinsu ko kuma su yi hasarar su, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Dr Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, babban sakataren hukumar ya bayyana hakan yayin wani karin haske da aka watsa a wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar.