Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin bayar da tallafin karatu ga daliban Najeriya a matakai daban-daban na ilimi idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Laraba yayin da yake ba da labarin tayin ilimi kyauta da ya bayar lokacin yana gwamnan jihar Kano.
Tsohon Ministan Tsaron ya ce irin wannan damar karatu zai kawo karshen koma bayan ilimi da kasar nan ke fuskanta yayin da ya yi Allah wadai da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta yi.
KARANTA ANAN: Gwamnatin tarayya ta Amince Katsinawa Su Rike Bindiga
Kwankwaso, wanda kwanan nan ya kaddamar da ofisoshin yakin neman zaben jam’iyyarsa a jihar Kebbi, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “Daya daga cikin abubuwan da na gada a matsayina na gwamnan Kano shi ne ci gaban da aka samu a rayuwar jama’armu.
“Wannan shi ne abin da muke da niyya a kai a matakin kasa wanda ko shakka babu zai kawo karshen koma bayan ilimi a yanzu. Ya kamata mu dawo da dalibanmu azuzuwa, ta yadda za a kare afkuwar lamarin kamar yadda wadannan daliban suka toshe hanyoyin shiga filin jirgin sama a kwanakin baya,” inji Kwankwaso.
A wani labarin kuma: Da Ɗumi-Ɗumi: Atiku Ya Rasa wani Mataimaki Na Kusa Dashi
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya rasa babban sakataren sa, Barr. Abdullahi Nyako.
Aminiya ta fahimci cewa Nyako ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis.
Ba a san abin da ya kai ga mutuwar hadimin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 ba.