By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan’sandan Nigeria reshen birnin tarayya Abuja, ta kama wani mai suna Musa Mukailu mai shekaru 18, da wani mai suna Damina Wali mai shekaru 17, bisa zargin su da garkuwa da mutane a kan mashigar Kwali dake Abuja.
Sanarwar ta fitone daga baki jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ASP Daniel Ndirpaya a ranar Alhamis a Abuja, in da yace wadanda ake zargin sun amsa da kansu cewa su mambobin masu garkuwa da mutane ne, inda suka hada kai dan suyi garkuwa da wasu mata guda biyu a kusa da mashigar Kwali.
Jami’in hulda da jama’ar ya ce suna iya kokarinsu wajen kare rayuwar jama’a da dukiyoyin mazauna birnin tarayya FCT, sannan ya bukaci mazauna birnin tarayya da idan suka ga wanda basu yarda da shi ba suyi gaggawar sanar dasu ta kan wadannan layu kan kamar haka, 0803200391, 0806158193, 0705733765, 0802894088.