By Abbas Yakubu yaura
Biyo bayan rikicin daya yi sanadin mutuwar dalibin kwalejin Dowen dan shekara 12, mahukuntan makarantar sun musanta ikirarin cewa an yi wa marigayin duka ne wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa har lahira.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwalejin Dowen ta bayyana cewa dalibin ya samu rauni ne a lokacin da yake buga kwallon kafa a ranar 21 ga watan Nuwamba 2021 kuma nan take aka ba shi agajin gaggawa kuma aka sallame shi a dakin kwanansa bayan ya nuna ya samu sauki.
Sannan Dalibin “Ya kasance a aji a ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba 2021, amma a lokacin makaranta wani abokinsa ya raka shi zuwa wurin karbar magani na Sick Bay inda ya koka da wani ciwo a kugunsa. Likitan ya duba shi kuma ya rubuta masa maganin Ibuprofen sabida ciwon, yayin da ma’aikacin jinya ya bashi kulawa, bayan haka ya dan sami sauki.
“A bisa ka’idar makarantar, likitan da ke wurin ya kira mahaifiyarsa inda ta kai rahoton faruwar lamarin inda ta bukaci ta zo wurinsa domin ya samu karin kulawa. Sai dai mahaifiyar tace ba ta Legas, ta yi magana kuma ta yi addu’a tare da shi ta wayar tarho, ta kuma yi alkawarin aika waliyin da ya dauke shi cikin gaggawa domin a ci gaba da kula da lafiyarsa.
“Lokacin da wakilin ya kasa zuwa, washegari ranar 23 ga watan Nuwamba, 2021, likitan ya sake kiran mahaifiyar kuma a wannan karon, ta ba da tabbacin cewa waliyinsa zai dauke shi daga makaranta.
Sai dai Hukumar ta ci gaba da bayanin cewa shugaban makarantar ya kuma zanta da mahaifiyar ta wayar tarho domin jin irin ci gaban da aka samu kuma “ta ba da rahoton cewa yana samun sauki sannan ta ba shi wayar domin ya tattauna da shugaban makarantar.
“Saboda haka, ba karamin abin mamaki ba ne a gare mu da muka karanta a shafukan sada zumunta na daji, har wasu dalibai suka yi masa dukan tsiya, kuma ya ambaci wasu sunaye. Nan da nan muka fara bincike kuma muka gayyato daliban da aka ambata don yin hira. Har ila yau, waliyin nasa ya kasance a wurin a yayin tattaunawar, wanda ya bayyana cewa babu wani abu da ya faru.
“Duk abin da ya faru ya kasance abin ban mamaki kuma ba a yarda da shi ba saboda: Makarantar tana da ingantattun tsare-tsare na hana cin zarafi kuma an bayyana sakamakon da ya dace ga dukan ɗalibai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Binciken farko ya nuna cewa babu wani fada, cin zarafi ko wani nau’in hari da aka kai wa yaron.