Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkar Soji Sanata Ali Ndume ya ce saba kudin tsarin mulkin Jam’iya ce a ce APC ta sake tsaida dan takarar shugabancin kasa daga yankin arewa maso gabas.
Dan Majalisar wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai ya bayyana haka ne a yayin wani taron musayar ra’ayi da kungiyar wakilan kafafen yada labarai karkashin kungiyar yan jaridu reshen birnin taryayya Abuja ta shirya.
Ya ce muddin aka yi yunkurin fitar da wani dan takara na shugabancin kasa a shiyar arewa maso gabas to babu shakka hakan wata kafa ce ta baiwa yankin wa’adi na uku bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin shi na biyu.
Sanata Ndume har wa yau ya ce a babin adalci shiyar kudu ce ke da damar fitar da dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ta APC.
Ndume ya ce “bana goyon bayan Jam;iyyar APC a ce ta fitar da dan takara daga arewa, kamata ya yi ta fitar daga shiyar kudu”.
“idan aka ce shiyar arewa ta fitar da dan takara to hakan na nuni da cewa shiyar za ta shafe wa’adi na uku kenan wanda kuma hakan ba adalci ba ne, ni kuma da ma na tsaya ne a kan gaskiya da adalci”
da ya tabo bangaren tsaro, Sanata Ndume ya bayyana rashin kayan aiki s matsayin kandagarki dake taka muhimmiyar rawa wajen kawo cikas ga rundunar da ke yaki da harkar ta tsaro.