Dalilin da yasa Ƴan Najeriya ke zuwa Ghana, Togo don neman ilimi – Farfesa Akande
Wani masani a fannin ilimi, Farfesa Busari Shaamsuddeen Akande ya bayyana cewa, muhalli mai aminci, da ake bukata na sana’o’i da samar da wutar lantarki na daga cikin dalilan da ya sa matasan Najeriya da iyayensu ke sa ido tare da zuwa kasashen Ghana da Togo domin neman ilimi mai zurfi duk da tsadar rayuwa.
Akande, Sakataren Majalisar Cibiyar Gudanarwa da Jagoranci na cibiyar ƙwararru kan ilimi ts Amurka, mai hedkwata a Jihar Kentucky ta Amurka, ya yi magana a wata hira da DAILY POST tayi da shi a Calabar ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ina Aiki Tukuru don Magance Rashin Tsaro – Soludo
“Wadannan ƙananan ƙasashe maƙwabta suna samar da matasa waɗanda suka kammala karatunsu tare da ƙwarewar da ake buƙata don tallafawa manyan masana’antu.
“A Togo ko Jamhuriyar Benin, babu batun yajin aiki. Akwai ingantacciyar wutar lantarki, muhalli mai aminci, zaman lafiya, ƙwararrun kwasa-kwasan jami’a.”
A nasa ra’ayin, Akande ya ce girman kasa ba shi da wata matsala idan ana maganar samun nasarar ilimi.
A cewarsa, idan kasa ta kasance karama, za ta iya murmurewa cikin sauri, ta bunkasa cikin sauri da kuma yin dukkan sabbin sauye-sauye cikin sauri.
Ya ce ya kamata manyan makarantu su zama na musamman ta yadda dalibai za su fito da kwarewa a fannonin da suka zaba.
“Ba inda daliban da suka kammala karatun shari’a a Jami’ar Noma da Makarantar Nazarin Shari’a ke samar da ƴan jarida ba.
“A Jamhuriyar Benin, kuna da jami’ar gudanarwa ta musamman don kimiyyar gudanarwa.”
Akande ya bayyana hanyoyin da kasar za ta iya jawo masu zuba jari a fannin ilimi domin rage dogaro da gwamnati.
A wani labarin kuma:
Shugaba Emmanuel Macron ya ce kasar Faransa za ta janye jakadanta tare da kawo karshen hadin gwiwar soji da Nijar bayan juyin mulkin da aka yi
Matakin dai ya biyo bayan nuna kyama da zanga-zangar adawa da kasancewar Faransa a kasar ta Nijar na tsawon watanni
Matakin na Macron ya zo ne sa’o’i bayan da jagororin juyin mulkin Nijar suka dauki mataki kan “jirgin Faransa”
Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta janye jakadanta tare da kawo karshen hadin gwiwar soji da Nijar bayan juyin mulkin da aka yi.
“Faransa ta yanke shawarar janye jakadanta. Nan da sa’o’i masu zuwa jakadan mu da jami’an diflomasiyya da dama za su koma Faransa,” in ji shugaban.
KARANTA WANNAN:Faransa Za ta Janye Sojoji da Jakadanta daga Nijar, Inji Macron
Ya kara da cewa hadin gwiwar soji ya kare kuma sojojin Faransa za su fice nan da watanni masu zuwa.
A ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji su kwace mulki a Jamhuriyar Nijar, inda suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.