Za’a Kammala Titin Abuja-Lagos a 2027 – Inji Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kammala aikin titin Abuja zuwa Legas nan da shekarar 2027.
Ministan ayyuka, Dave Umahi, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Legas ranar Asabar, ya bayyana cewa, shirin titin mai tsawon kilomita 470 zai dauki tsawon shekaru 100 ana cin gajiyar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Faransa Za ta Janye Sojoji da Jakadanta daga Nijar, Inji Macron
Ya kuma bayyana cewa, titin da wata kungiya mai zaman kanta za ta gina ba tare da biyan kudin Gwamnatin Tarayya ba, zai bi ta Kogi, Ekiti, Oyo, Legas, Ogun, Neja, Kwara, da Babban Birnin Tarayya, FCT.
Ya kara da cewa: “Da yawa masu shakka suna cewa ‘ba shi yiwuwa lokacin da na fara gabatar da wannan ga jama’a. Wannan shine sabon fata na shugaba Tinubu.
“Shugaban kasa ya amince da na gaggauta aiwatar da wannan aikin. Wannan aikin zai kasance hanyoyi biyu ne, amma kowace hanya za ta zama hanya mai hawa biyu, kuma zai zama mita 14.
“Tsarin rayuwa na wannan babban titin zai kasance shekaru 100 kuma za a kammala shi cikin shekaru hudu. Ba zamu bada ko kobo don aikin ba.
A wani labarin kuma:Dalilin da yasa Ƴan Najeriya ke zuwa Ghana, Togo don neman ilimi – Farfesa Akande
A nasa ra’ayin, Akande ya ce girman kasa ba shi da wata matsala idan ana maganar samun nasarar ilimi.
A cewarsa, idan kasa ta kasance karama, za ta iya murmurewa cikin sauri, ta bunkasa cikin sauri da kuma yin dukkan sabbin sauye-sauye cikin sauri.