Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya ki nada dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa a lokacin da aka bukaci ya yi hakan,kamar yadda The Nation ta rawaito.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa sau uku ina tsayawa neman takarar shugaban kasa kuma na kare a kotun koli ba tare da samun nasara ba sannan na yi nasara a karo na 4 ta hanyar dimokuradiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsananin Kishi: Wani Magidanci Ya Sheke Tsohuwar Matarsa da Tabarya
Bisa hakanne yake mamakin dalilin da ya sa zai nada dan takarar shugaban kasa a tsarin dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa Marigayi Ahmadu Bello ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da adalci a matsayinsa na shugaban kasa ya kuma tsaya akan kyawawan halayen.
Buhari ya bayyana hakan ne jiya a garin Lafiya yayin taron tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara ta 2023 wanda gwamnatin jihar Nasarawa tare da hadin gwiwar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation suka shirya.
Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bukaci ‘yan Najeriya da su amince da sakamakon zaben, inda ya shawarci mutanen da suka yi zabe da su nemi hakkinsu a kotu.
Ya ce Marigayi Sardauna, Sir Ahmadu Bello, ya jajirce wajen ganin an samu hadin kai, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya, kuma ya tsaya tsayin daka har zuwa rasuwarsa, ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi sadaukar da kai da kuma abubuwan da ya bari.
Babban bako, a wajen taron tunawa da Sir Ahmadu Bello karo na 9 wanda Farfesa Patrick Lumumba na kasar Kenya ya gabatar da taken ‘sahihin zabe a matsayin mafita na neman ingantaccen shugabanci da gadon mulki nagari da al’adun dimokaradiyya mai dorewa a Najeriya’.
Gwamnan Jihar Filato kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Bako Lalong ya jajirce wajen neman mulki ya koma Kudu domin tabbatar da adalci wanda daya ne daga cikin kyawawan halaye da marigayi Ahmadu Bello ya tsaya a kai.
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, wanda shi ne babban mai masaukin baki, ya gode wa Farfesa Lumumba bisa amsa karramawar da suka yi daga Kenya da sauran gwamnonin Arewa da kuma baki da aka gayyata.
Taron tunawa da Sardauna karo na 9 ya samu halartar shugabanta kuma tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da sauran tsofaffin gwamnoni kamar Murtala Nyako na Adamawa, Idris Abubakar na Kogi, Sanata Tanko Al-Makura da Abdullahi Adamu na jihar Nasarawa da dai sauransu.
A wani labarin kuma, Hatsarin Jirgin Max Air: NSIB, NCAA Sun Shirya Gudanar Da Cikakken Bincike
Hukumar NSIB da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) sun bayyana shirin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin fashewar tayoyin jirgin saman Max Air.
Hadarin ya afku ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe (NAIA) dake Abuja, ranar Lahadi.