Dalilin da yasa wutar lantarkin Mambilla bai samu wani kaso a kasafin kudin 2024 – Ministan Tinubu
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana dalilin da ya sa aikin wutar lantarki na Mambilla bai samu wani kaso ba a cikin kudirin kasafin kudin 2024 na ma’aikatar.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani zama da kwamitin hadin gwiwa na kwamitin majalisar dattawa da na wakilai kan harkokin wutar lantarki karkashin jagorancin Sanata Enyinnaya Abaribe, suka gudanar ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rikicin Rivers: Ka Ayyana kujerun ‘Yan Majalisa 27 a Matsayin Babu Kowa – LP Ga Shugaban Majalisa
Ya ce ana ci gaba da tafka muhawara a kan shari’ar aikin Mambilla, don haka ba a kayyade aikin
Kamfanin Sunrise Power and Transmission a ranar 10 ga Oktoba, 2017, ya maka gwamnatin tarayya zuwa kotun kasa da kasa da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa da kasa da ke birnin Paris na kasar Faransa bisa zargin karya kwangilar da aka kulla a shekarar 2003 na gina wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050 a shekarar 2003. Kamfanin a Mambilla, Jihar Taraba, a kan Gine-gine, Aiki da Canji a kan $6bn.
Gwamnatin Tarayya, a nata bangaren, ta dage cewa bayar da kwangilar ba bisa ka’ida bane.
Adelabu ya shaida wa Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai cewa da gangan ya cire aikin Mambilla daga kudirin kasafin kudin 2024 na ma’aikatar.
Ya ce, “Ga Mambilla, babu tanadi a 2024. Ba kuskure ba ne. Da gangan ne. Yana ƙarƙashin hukunci na ƙasa da ƙasa. Har sai an warware shi, ba za mu iya yin komai a kai ba.”
Ya ce kamfanin na Zungeru zai fara aiki a watan Disamba.
“Kashi 99.8 cikin 100 na aikin samar da wutar lantarkin a shirye yake. An kusa kammalawa kuma muna da niyyar fara aiki a bana.
A wani labarin kuma:Yan Najeriya na kokawa kan ƙarancin takardun Naira a fadin kasar
Kwanaki kadan ga bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, ‘yan Najeriya sun sake fuskantar karancin kudin Naira.
Wannan ci gaban na zuwa ne duk da tabbacin da babban bankin Najeriya, CBN ya bayar na samun takardar kudin.