Dalilin Kammala Jigilar Alhazan Jihar Kwara Da Wuri
Kimanin alhazai 3,550 daga jihar Kwara da suka yi aikin hajjin shekarar 2023 a kasar Saudiyya sun dawo gida.
Kashi na karshe na alhazan sun isa filin jirgin sama na Ilorin da karfe 9 na safiyar ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN:To Fa: An Kame Wata Amarya Bisa Zargin Ta da Yankewa Angonta Kayan Aiki
Jirgin da ya yi jigilar sauran alhazan jihar Kwara 272 ya tashi daga filin jirgin sama na Jeddah na kasar Saudiyya da misalin karfe 2:30 na safiyar Asabar.
Dukkanin mahajjatan sun kasance cikin farin ciki kuma sun samu tarba daga ‘yan uwansu da masu fatan alheri.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji AbdulSalam AbdulKadir, wanda ya isa tare da wasu, ya ce mahajjata 272 ne ke cikin jirgin.
Ya tabbatar da cewa jihar ta samu mutuwar mutum daya mai suna Alhaji Busari Alao, daga Ilorin wanda ke da shekaru 70 a duniya.
A wani labarin kuma:Ta Leko Ta Koma: Gwamna Zulum Ya Janye Ngoshe Daga Jerin Sunayen Kwamishinoni
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya janye sunan Dakta Ibrahim Yusuf Ngoshe a matsayin kwamishina.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau shine wanda ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa adadin wadanda aka nada a matsayin kwamishinoni ya ragu daga 18 zuwa 17.