Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya janye sunan Dakta Ibrahim Yusuf Ngoshe a matsayin kwamishina, Daily Post ta rahoto.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau shine wanda ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa adadin wadanda aka nada a matsayin kwamishinoni ya ragu daga 18 zuwa 17.
KARANTA WANNAN: To Fa: An Kame Wata Amarya Bisa Zargin Ta da Yankewa Angonta Kayan Aiki
Matakin na Zulum na kunshe ne a cikin wata wasika da ya rubutawa majalisar dokokin jihar Borno a yammacin ranar Juma’a.
Gwamna Zulum, kamar yadda sanarwar ta bayyana, a ranar Juma’a, 28 ga watan Yuli, 2023, ya mika wa majalisar sunaye 18, ciki har da na Ngoshe, wanda sunansa yake ana 13.
A wani labarin kuma,Rasha: Najeriya Zata Sake Yin Aiki a Karkashin Shugaba Tinubu, Shettima Ya Tabbatar
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya musamman mazauna kasar Rasha cewa kasar karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta samu canji mai kyau da ci gaba.
Ya ba da wannan tabbacin ne yayin wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna birnin St. Petersburg na kasar Rasha.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya gana da su a yammacin ranar Juma’a, ya yi jawabi kan matsalolin da al’ummar suka nuna.
Ya ci gaba da cewa, “Ku tabbata a cikin watanni 9 zuwa 12 masu zuwa, za a samu sauyi cikin sauri a arzikin Nijeriya. Ina magana ne da dukkan ma’ana da kuma alhaki saboda na yi imani da iyawa da jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
A cewar wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola ya fitar ranar Asabar, yace Shettima ya yi magana game da kokarin da gwamnatin ke yi na sake farfado da tattalin arzikin kasar.
Sannan “Ya kuma jaddada aniyar kammala ginin katafariyar masana’antar karafa ta Ajaokuta da kuma farfado da Kamfanin Aluminium Smelter Company of Nigeria (ALSCON).