Wata kotun Dei-Dei mai daraja ta daya da ke Abuja ta yanke wa wani matashin babur mai shekaru 22, Aron Sunday, hukuncin watanni 10 a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin satar dukiyar da ta kai Naira 700,000.
Sunday, wani mazaunin Dutse Jabu da ke Abuja, an yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifuffuka uku da ake tuhumarsa da su, da suka hada da fasa gida da sata.
Karanta nanKotu Ta Garkame Asusun Bankin Jahar Oyo Saboda Dumbin Bashi
Sai dai alkalin kotun, Saminu Suleiman, ya baiwa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N40,000, sannan ya umarce shi da ya biya N700,000 ga wanda ya shigar da kara.
Alkalin kotun ya gargadi mai laifin da ya kasance mai halin kirki kuma ya daina aikata laifuka bayan ya kammala zaman gidan yari.
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Chinedu Ogada, ya sanar da kotun cewa mai shigar da kara, Fagbemi Peter da Yemi Ayeni, dukkansu mazauna Dutse Jabu, Abuja ne suka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Dutse Alhaji a ranar 12 ga watan Nuwamba.
A cewarsa, a daidai wannan rana da misalin karfe 4:00 na safe, wanda aka yankewa laifin ya kutsa kai cikin harabar mai karar ta hanyar tsallake shingen dakin kwanansa ta silin, amma aka kama shi.
Ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya shiga gidan mai karar ne sau biyu a baya kuma ya kwashe akwatin ajiyarsa mai dauke da Naira 300,000,wayoyi na lantarki, socket na lantarki, injin famfo da fitilar bango, wadanda kudinsu ya kai N700,000.
A wani labarin kumaYan Bindiga Sun Kashe Malamin Makaranta Bayan Karbar Miliyan 2 A Jahar Zamfara
Mai gabatar da kara ya ce bayan wani lokaci a cikin watan Oktoba, wanda aka yankewa hukuncin da sauran su a halin yanzu su ma sun je shagon Ayeni suka sace mata wayar Tecno pop7 da wata jaka mai dauke da N120,000.
A cewar mai gabatar da kara, wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa ne a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike da bincike.
Laifukan sun saba wa sashi na 348 da 288 na kundin laifuffuka.