Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malami a Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara da ke Maru, Malam Nasiru Mohammed Anka, bayan sun karbi Naira miliyan 2 na kudin fansa domin ’yancinsa.
DAILY POST ta tattaro cewa an yi garkuwa da Anka ne a gidansa da ke garin Maru a karamar hukumar Maru a jihar makonni uku da suka gabata.
Karanta nanKotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Karar Da Aisha Binani Ta Shigar
An kuma bayyana cewa, an yi garkuwa da malamin ne tare da wasu mazauna garin a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa garin tare da yin garkuwa da mutane da dama.
Wani mazaunin yankin mai suna Usman Ibrahim ya tabbatar da kashe malamin.
A cewarsa, wata mata da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su a wani wuri daban amma ta tsere makonni bayan da aka yi garkuwa da ita ta shaida wa mutane labarin rasuwar malamin.
Matar ta ce an kashe Nasiru Muhammad Anka a gabanta ne biyo bayan azabtarwa da ‘yan bindiga suka yi a sansaninsu bayan da iyalansa suka kasa biyan kudin da masu garkuwa da mutane suka nema domin neman ’yancinsa.
Ta ce ta tsere daga sansanin ‘yan fashin ne a lokacin da suka bugu sannan suka yi barci, inda ta ce bayan kwana biyu da rasuwar malamin, ‘yan fashin sun yi kokarin cire masa wasu sassan jikin sa, amma suka tsaya a lokacin da suka gano cewa tuni gawar tasa ta lalace.
A wani labarin kumaA Shirye Nake In Rasa Raina Akan Kasata-Peter Obi
‘Yan fashin sun rika gaya masa cewa mutanensa suna da kudi, idan suna sonsa su kawo kudin ko kuma su kashe shi, kuma a haka ne suka kashe shi bayan sun karbi Naira miliyan biyu da suka ce bai isa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abdulahi, ba a samu jin ta bakinsa ba bayan yaki daukar kiran da aka yi masa.