An kashe wani Jami’in dan sanda a jihar Bauchi mai suna Mukhtar Ibrahim.
Wasu yan yan bindiga ne dai da ba a san ko su wanene ba suka kashe Mukhtar Ibrahim tare da abokin shi yayin dqa suke wani sintiri a kan hanyar Nabordo dake karamar hukumar Toro.
Abokin nashi mai suna Uba Samaila da ne ga mai gudnumar Nabardo.
Kakakin rundunar Yan sandar jihar Bauchi Ahmad Wakili ya tabbatar da aukuwar al’amarin inda ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar asabar.
Ya kara da cewa tuni Kwamishinan Yan Sandar Jihar ya bada umarnin girke jami’an yan sanda a yankin.
Idan za a iya tunawa dai kimanin yan sanda goma ne suka rasa rayukan su a bakin aiki cikin makonni biyu kachal.