Dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Adamawa, Ijiniya Umar Mustapha, ya yi watsi da bukatarsa ta tsayawa takara inda ya goyi bayan takwararsa ta jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Binani.
Umar Mustapha, wanda aka fi sani da Otumba, ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai a Yola da yammacin ranar Lahadi, inda ya ce biyo bayan kalubalen da ya sha fama da shi wajen neman zama gwamna, ya yanke shawarar dakatar da wannan buri tare da marawa burin Binani don cikar burinta na zama gwamna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sakamakon Zaben 2023: Takaddar Shedar Lashe Zabe Ta INEC Kamar Gasar Cin Kofin Duniya Ne – Tinubu
Ya ce, “Ina da yakinin cewa Binani zata samar da shugabanci na gari wanda zai ba da fifiko ga jarin dan Adam da bunkasa albarkatun da za su ci gaba da bunkasa jihar Adamawa.
“Don haka nake kira ga dukkan magoya bayana da su fito a ranar Asabar 11 ga watan Maris, su zabi mai girma Sanata Aishatu Ahmed Binani a matsayin gwamnan jihar Adamawa.”
Ya kara da cewa yana sanya duk wani tsari na kungiyar yakin neman zaben sa na Otumba a hannun Binani.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa Otumba wanda ya dade yana nesa da shugabancin jam’iyyarsa ta Labour a matakin jiha da kasa, ya bayyana amincewar Binani ne a kan sa.
Ya dade ba ya aiki da jam’iyyarsa ta Labour, kuma a kwanakin baya ya rika zargin shugabannin jam’iyyar na jihar da yin aiki tare da jam’iyyar PDP reshen jihar domin samun nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri a zaben da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris.
Umar Mustapha dai daf da zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Tinubu, wanda yanzu shi ne zababben shugaban kasa, inda ya bayyana cewa ba shi da wata alaka tsakaninsa da Peter Obi na jam’iyyar Labour domin tallata takararsa.
Umar Mustapha bai fayyace ba a taron na ranar Lahadi idan ya bar jam’iyyar Labour; kamar yadda a dabara ya bar wannan bangaren daga cikin amsoshin tambayoyin da ‘yan jarida suka yi masa.
Sanata Aishatu Binani da ta halarci taron takaitaccen biki da Umar Mustapha ya bayyana amincewarsa gareta, ta ce abin farin ciki ne kuma hakan zai kara mata karfin gwiwa a zaben na ranar Asabar mai zuwa.
A wani labarin kuma, Nasarar Tinubu: PDP Na Kokarin Tada Zaune Tsaye A Najeriya Tare Da Zanga-Zangar Abuja – Fani-kayode
Wani jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, ya zargi jam’iyyar PDP, da kokarin tada zaune tsaye ga ‘yan Najeriya a zanga-zangar da zasu yi a Abuja, kan rashin nasarar da jam’iyyar ta yi a zaben shugaban kasa.
Fani-Kayode ya ce jam’iyyar APC a shirye take da abin da PDP ke shiryawa.