Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ba shi tamkar gasar cin kofin duniya ne, Daily Post ta rawaito
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara fadar Sarkin Legas, Rilwan Akinolu, ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nasarar Tinubu: PDP Na Kokarin Tada Zaune Tsaye A Najeriya Tare Da Zanga-Zangar Abuja – Fani-kayode
Tinubu, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar APC, an bayyana shi ne a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Da yake jawabi a fadar, Tinubu ya ce: “Tafiyar da muka yi, mun dawo gida da takardar shedar lashe zabe.
“Kamar gasar cin kofin duniya ce tamu kuma na gode muku da kokarinku.”
A wani labarin kuma, Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Lalata Gidaje 105 a Jihar Ekiti
Ruwan saman da ya biyo bayan iska da aka shafe sa’o’i biyu ana yi a yammacin Juma’a ya lalata gine-gine 105 a Oke-Ako da ke karamar hukumar Ikole ta jihar Ekiti.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa ruwan saman ya lalata cibiyoyin wutar lantarki a fadin garin, lamarin da ya jefa mutanen cikin duhu.