Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeke Ihedioha, ya janye daga takara a zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Janyewar Ihedioha ta biyo bayan abubuwa da dama da suka faru a jam’iyyar PDP, waɗanda suka sanya aka tumɓuke shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu, daga muƙamin sa.
KU KARANTA KUMA: “Ka rufamin asiri kada ka bar ni”, Budurwa ta koma roƙon saurayin ta, hirar su ta bayyana
Ihedioha yayi aiki a ƙarƙashin Ayu a matsayin kakakin watsa labaran sa lokacin yana shugaban majalisar dattawa a shekarar 1992.
Wakilin Daily Trust ya samo cewa Ihedioha ya sanar da janyewar sa daga takarar ne a wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya janye daga takarar ne domin hakan shine abinda yafi zama alkhairi ga jam’iyyar.
Da aka tuntuɓi hadimin sa, Chibuike Onyeukwu, ya tabbatar da janyewar sa daga takarar amma bai yi wani ƙarin bayani ba.
Jam’iyyar PDP dai ta shirya gudanar da zaben fidda gwani na gwamnan jihar Imo a ranar 15 ga watan Afrilun 2023.
Zababben Gwamnan Kwara Da Wasu Sun Karbi Takardar Shaidar Lashe Zabe
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara a ranar Talata ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Ilorin babban birnin jihar, yana mai tabbatar wa da jama’a cewa zai ci gaba da mai da martani da jin dadin sha’awar ‘yan kasa kamar yadda ya saba.
Da yake jawabi a wajen taron, ga Kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Kogi, Kwara da Neja, Farfesa Sanni Muhammed Adam SAN, ya ce zabukan da suka gabata za su shiga tarihi a matsayin na daya daga cikin zabukan da aka taba gudanarwa a Najeriya.