Daga: Rabilu Sanusi Bena
- Manchester United na neman Mai tsaron ragar Inter Milan dan asalin kasar Kamaru Andre Onana
- Dan wasa Mason Greenwood ba zai bar Manchester United ba a bana duk da dakatarwar da aka yi masa
- Dan wasa Ikay Gundogan zai bar Manchester City Bayan lashe kofuna uku a kakar bana
A yayin da kasuwar saye da sayarwar Yan wasa ta bude manyan kungiyoyin Turai na ta faman shige da fice domin ganin sun samu damar daukar Yan wasan da suke ganin zasu taimaka masu ainun a kakar wasa ta badi
Manchester United na neman Mai tsaron ragar Inter Milan dan asalin kasar Kamaru Andre Onana yayin da Kwantiragin Mai tsaron raga David Degea ke gab da karewa @themirror
KARANTA WANNAN: Musaya: Man City Ta Sanya ‘Yan Wasanta 6 A Kasuwa
Kai Harvertz ba na sayarwa bane inji Chelsea yayin da kungiyoyi kamar Real Madrid dake Sifen da Kuma Manchester United ta Ingila ke nemansa @the mirror
Mason Greenwood ba zai bar Manchester United ba a bana duk da dakatarwar da aka yi mishi bayan samunsa da laifin yunkurin yin fyade @ thesun
Ikay Gundogan zai bar Manchester City Bayan lashe kofuna uku a kakar bana, kungiyar ta lura cewar Dan wasan na Jamus ya fara tsufa Wanda hakan ka iya hanashi yin kokari kamar yada ya saba @telegraph
Joao Cancelo dake zaman aro a Bayern Munchen ta kasar Jamus daga Manchester City na fatan zuwa Real Madrid a badi duk da shaawar daukarsa da Barcelona tayi
A wani labarin kuma, Chelsea Zata Dauko Dan Wasa Caicedo Akan Kudi Kusan Yuro Miliyan 100
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shiga wata fafutuka, a kokarin da ta ke yi karkashin jagorancin mamallakin kungiyar Todd Bohely na dawo da kungiyar cikin hayyacinta bayan kammala kakar bana
Chelsea ta taya matashin dan wasan baya na kungiyar Brighton Hove Alboin Moses Caicedo akan zunuzurutun kudi har Yuro Miliyan 80.