- Wani magidanci mai shekaru 50, Mukhtar Ibrahim ya roki kotun shari’a da ta taimaka ta rabashi da tsohuwar matarsa, Sa’adatu Abdulhadi
- Da kyar nasha lokacin da ta taɓa kiran danginta don su yi mini dukan tsiya, don haka ta bar ni da tarin raunuka
- Ya mai shari’a ba na iya barci da idona biyu a rufe don gudun abinda zai faru tunda ta ki barin gidana
Wani magidanci mai shekaru 50, Mukhtar Ibrahim ya roki kotun shari’a da ke zamanta a Kaduna da ta kori tsohuwar matarsa, Sa’adatu Abdulhadi daga gidansa.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, wanda ya shigar da karar wanda ya yi rokon ta bakin lauyansa, Jamilu Sulaiman ya kuma roki kotun da ta tabbatar da sakin aure na uku da ya yi wa wanda ake kara.
KARANTA WANNAN: Rashin Tausayi: Mijina Yana Lakadamun Dukan Tsiya, Yana Barazanar Hallaka Iyayena— Matar Aure
“Ina kuma son na kula da ‘ya’yana hudu saboda ba ta da tarbiyya. Ta taɓa kiran danginta don su yi mini dukan tsiya, don haka ta bar ni da tarin raunuka.
“A yanzu, ni mai tsarki ne a rayuwata kuma ba zan iya barci da idona biyu a rufe ba tunda ta ki barin gidan,” in ji shi.
Sai dai kuma wancce ake karar ba ta samu hakartar kotun ba amma dan sakon kotun ya tabbatar da yi mata hudubar kotun.
Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Yuli.
A wani labarin kuma, Musaya: Man City Ta Sanya ‘Yan Wasanta 6 A Kasuwa
Yanzu haka dai Manchester City na neman cefanar da akalla manyan ‘yan wasanta shida
Man City ta zama kungiyar Ingila ta farko tun bayan Manchester United a kakar wasa ta shekarar 1998-99 da ta lashe kofuna uku
Barcelona na zawarcin uku daga cikin wadannan ‘yan wasa