Adadin danyen man da Najeriya ta siyar ya karu da kashi 46.41 zuwa Naira tiriliyan 21.09 a shekarar 2022 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 14.41 a shekarar 2021, a cewar sabon rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS.
Bayanai sun nuna yadda jimillar kasuwancin man a Najeriya ya tashi da kashi 31.79 wato daga N39.75tn a shekarar 2021 zuwa N52.39tn a shekarar 2022; a don haka, danyen man ya kai kashi 78.74 cikin 100 na jimillar danyen man da aka fitar.
KU KARANTA: Kwankwaso Ba Shugaban Kanawa Ba Ne ~ Bashir Elrufa’i
Jimillar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a shekarar 2022 ya karu da kashi 41.72 cikin dari, wato dai daga N18.91tn a shekarar 2021 zuwa N26.79tn a shekarar 2022.
Kuma Yawan kayayyakin da aka shigo da su ya karu da kashi 22.77 cikin dari daga N20.84tn a shekarar 2021 zuwa N25.59tn a shekarar 2022.
Alkaluman hukumar ta NBS sun nuna cewa kasashen Spain, Netherlands, Indiya, Faransa da kuma Indonesiya ne suka kasance kasashe biyar da suka fi karbar kayan da Najeriya ta fitar da su.
Yayin da kuma, kasashen China, Belgium, India, Netherlands da Amurka suka zama kasashe biyar da ke kan gaba wajen shigar da kayayyakin su zuwa Najeriya, wanda darajarsu ta kai Naira tiriliyan 2.99.
A wani labarin kuma: An Sanya Ranar Da Neymar Zai Bar Asibiti, Bayan An Masa Tiyata
Tauraron dan kwallon Brazil Neymar zai bar asibitin wasanni na Qatar a ranar Lahadi don hutawa kafin ya fara gyara bayan an yi masa tiyata a idon sawunsa, in ji jami’ai.
Likitoci a asibitin Aspetar ba su bayar da ranar da dan wasan Paris Saint-Germain mai shekara 31 zai dawo taka leda ba amma suna da yakinin cewa tiyatar da aka yi ranar Juma’a ta yi nasara.