Bashir, dan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya yi hasashen cewa Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, zai zama shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaba, Daily Post ta rawaito.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya yabawa Kwankwaso kan sakamakon zaben shugaban kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Yi Wa Wasu Ƴaƴan Jam’iyyar PDP Ɗaurin Goro
Kwankwaso ya zo na hudu a zaben shugaban kasa da aka kammala a bayan Peter Obi na jam’iyyar Labour, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Bola Tinubu na jam’iyyar, APC.
A lokacin zaben, Kwankwaso ya fi samun kuri’u a jihar Kano, lamarin da ya sanya wasu masu suka suka bayyana shi a matsayin “Shugaban Kano”.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bashir ya rubuta cewa: “Wadanda suke yiwa Kwankwaso dariya cewa shi ne shugaban jihar Kano kadai ba za su yi dariya ba nan da ‘yan shekaru. Shi ne Buhari na gaba, mai yiwuwa.”
A wani labarin kuma, Sanata Barau Jibrin Ya Bukaci Masoyansa Suyi APC Sak
Yanzu haka dai babban mai taimakawa sanatan Kano ta Arewa Barau Ibrahim Jibrin kan kafafen sada zumunta Malam Basiru Yusuf Shuwaki ya mayar da martani kan kalaman maimagana da yawun AA Zaura Hon. Dahiru Maihuddadu, Kamar yadda Freedom Radio ta rawaito.
Idan dai za’a ita tunawa Maihuddadu ya bayyana cewa sun je wani taro inda aka basu makudan kudade don su yaki takarar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da sunan Sanata Barau Jibrin.