Daruruwan ‘yan ta’addar Boko Haram da ke tsare a wani sansani a jihar Borno bayan sun mika wuya ga sojoji sun tayar da tarzoma a ranar Larabar da ta gabata domin neman hakkin naman shanu Lamar yanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito a rahotansa.
Rikicin dai ya sanya mazauna Maiduguri kawanya a sansanin, suna rike da takubba, wukake da kulake, tare da yin barazanar kashe duk wanda ya bar sansanin, in ji majiyoyin tsaro.
Lamarin dai ya bayyana wani muhimmin aiki da hukumomi ke fuskanta na sake shigar da tsaffin mayaka cikin al’ummomin da suka sha fama da hare-hare da sace-sacen shekaru a tsawon shekaru 12 na rikicin masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama.
Rundunar soji ta gabatar da mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram da iyalai a ‘yan watannin nan a matsayin alamar nasarar kawo karshen rikicin da ya barke a arewa maso gabashin jihar Borno, amma har yanzu mazauna yankin na kallonsu a matsayin hadarin tsaro.
Kimanin ‘yan Boko Haram 250 da suka hada da mata da kananan yara ne suka gudanar da wata zanga-zanga mai zafi a unguwar Gidan Taki da ke wajen birnin, inda suka farfasa tagogi da kofofi tare da yin barazanar ficewa daga sansanin idan har ba a biya musu bukatarsu ba, in ji majiyoyin da mazauna yankin.
“Yan Boko Haram din sun kai farmaki da safiyar yau, inda suka karya kofa da tagogi har ma sun yi yunkurin barin sansanin,” in ji Konto Garga, wani ma’aikacin Civilian Joint Task Force da ke taimaka wa sojoji.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito rundunar sojin Najeriya na cewa, mayakan Boko Haram 18,000 da iyalansu ne suka mika wuya ga sojojin kasar bayan mutuwar shugabansu Abubakar Shekau a watan Mayu.
Shekau dai ya tarwatsa kansa ne domin gudun kada a kama shi a lokacin da suke fafatawa da babbar kungiyar su ta ISWAP a dajin Sambisa.
Kungiyar ta ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016 inda ta zama babbar kungiya a Najeriya da ke da alaka da kungiyar da ake kira daular Islama.
Da yawan mazauna Maiduguri na fargabar cewa Boko Haram na mika wuya ne ba don nadama ba, sai dai don gudun gujewa abokan hamayyar ISWAP da ke aiwatar da hukuncin kisa kan mayakan Boko Haram saboda kin mika wuya ga kungiyar.
Majiyoyin sun ce ‘yan ta’addan da ke zanga-zangar, wadanda suka kasance a sansanin tun a watan Augusta, suna neman hukumomi su mika musu saniyar da ake ba su kowace rana domin su yanka da kansu a maimakon a ba su naman sa.
“Mutanen da ke zaune a yankin sun fito da makaman da aka kera a cikin gida kuma suka sha alwashin kashe duk wani daga cikin masu zanga-zangar da ya fita daga sansanin,” in ji wani dan kungiyar ‘yan bindiga Garga.
“Mutane har yanzu suna kallonsu a matsayin barazana ta tsaro,” in ji Garga, wanda yana cikin jami’an tsaro da aka tura domin hana mayakan jihadi ficewa.
Wani mazaunin Gidan Taki Usman Bunu ya ce mutanen yankin ba su yarda da gaske ne wadanda suka mika wuya ba kuma zanga-zangar ta tabbatar da zarginsu ne kawai.
“Har yanzu suna daukar duk wanda baya cikin su a matsayin kafiri, shi ya sa suke son a bar su su yanka saniyar su da kansu. Da sun fito daga sansanin da ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kammalawa da su duka saboda mun san hadarinsu,” in ji shi.
Barazanar mutanen da ke dauke da makamai da kuma taimakon jami’an tsaro ne ya kawo karshen tarzomar kuma fursunonin sun koma matsugunin su, in ji Bunu.
Rikicin dai shi ne karo na biyu a sansanin, inda aka samu irin wannan tarzomar a cikin watan Satumba, in ji shugaban Civilian JTF, Babakura Kolo.
Fursunonin na Boko Haram dai tun lokacin da suka isa sansanin sun kasance cikin rashin da’a, inda suke ta rigima da mutanensa da ke gadin sansanin, tare da zarginsu da kallon matansu, in ji Kolo.
Kolo ya ce “Har yanzu suna da tunanin Boko Haram kuma suna zargin mutanen mu a matsayin wakilan gwamnatin kafirci.”