By Abbas Yakubu Yaura
Kwanaki shida bayan harin daya yi sanadin mutuwar wani Janar da wasu jami’an sojojin Najeriya uku a garin Chibok da Askira Uba dake kudancin Borno, Damboa, wata karamar hukumar dake makwabtaka da ita a halin yanzu tana fama da munanan hare-hare daga ‘yan ta’addan jihadi dake yankin yammacin Afirka.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wannan hari dai shi ne na uku a cikin wata guda a garin Damboa.Duk da cewa rahotanni na da tsarin bayanai da aka samu har zuwa lokacin hada wannan rahoto sun nuna cewa maharan sun zo garin ne da sanyin safiyar Juma’a da misalin karfe 5:30 na safe kuma a halin yanzu suna kona gidaje da dukiyoyin jama’a wadanda basu ji ba basu ganiba.
Har yanzu dai babu rahoton hasarar rayukan jama’a amma Damboa na daya daga cikin garuruwan da ‘yan ta’addar suka fi tsananta kai farmaki duk da kusancinsa da Sambisa da kuma fuskantar hare-hare da dama daga ‘yan ta’addar ISWAP.