Declan Rice ya bayyana dalilin da yasa ya zaɓi Arteta akan Guardiola
Dan wasan tsakiya na Arsenal Declan Rice ya bayyana cewa kocin kungiyar Arsenal Mikel Arteta ya taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawararsa ta komawa kungiyar Arsenal ɗin maimakon kungiyoyin Manchester City da Chelsea da Manchester United da suka dade suna zawarcinsa.
Gunners din ta doke abokan karawarta na gasar Premier league wajen ɗaukar ɗan wasan, inda suka kulla yarjejeniya da Rice kan kudi fan miliyan 105 daga West Ham.
A wani lokacin bazara bayan kammala kakar da ta gabata, an yi imanin cewa Manchester City ce ke kan gaba wajen siyan Rice musamman ganin cewa ta lashe kofuna uku a karkashin koci Pep Guardiola.
Sai dai dan wasan mai shekaru 24 ya bayyana cewa fatan yin wasa a karkashin Arteta shine babban burin sa kuma abin da ya biyo bayan komawarsa arewacin Landan kenan wato Emirates.
KARANTA NAN:An kafa kwamiti domin bincikar wasu manyan Makarantu bisa zargin karkatar da kuɗaɗe
Rice ya shaida wa gidan talabijin na Channel 4 cewa “ina ganin tun lokacin da na hadu da koci Mikel Arteta ya san cewa shi ne wanda nake so in yi aiki da shi a matakina na gaba wajen harkar kwallon kafa.
Kamar yadda Rice ya ce, “ta la’akari da yadda Arteta ya laƙanci kwallon kafa, da yadda yake son buga kwallon kafa, ina ganin mun ga yadda kungiyar ta Arsenal ta ke buga wasa a shekaru biyun da suka gabata, yadda suke taka leda cikin salon ƙwarewa da nuna hazaƙa, ina ganin
ni kaina ya fi dacewa da Ni in shiga kungiyar.
Kungiyoyi da dama a gasar Premier ta kasar Ingila sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasa Declan Rice daga tsohuwar kungiyar shi wato West Ham, a shekaru biyu da suka gabata.
Kungiyar Manchester United da Chelsea sun shiga cikin masu neman dan wasan a lokuta daban-daban amma Kocinsa David Moyes ya nace akan dan wasan sai ya kai Euro miliyan 100 kafin kungiyoyin su samu damar daukar shi.
A karshen kakar wasan da ta gabata ne Manchester City ta nuna sha’awa akan dan wasa, inda kuma ake ganin kungiyar ta fi dacewa da ta dauke shi duba da yadda take kan ganiya, amma daga karshe Declan Rice ya tafi zuwa Arsenal akan kuɗi Euro miliyan 105.